Fassarar mafarkin Gaisawa da Makiyi: Malaman Fassarar mafarki sun ce in mutum yayi mafarkin yana gaisawa da makiyin shi mafarkin yana nuna soyayya zata shiga tsakanin su. Sun dogara ga nassin Hadisi Manzon Allah Yace “Kuyi musafa da junan ku sai soyayya ta karu.” Saboda haka suka ce gaisawa da makiyi yana nuna soyayya zata shiga tsakanin ku.
Fassarar mafarkin tumaki: Malaman fassarar mafarki sun ce idan mutum yayi mafarkin ya mallaki garden tumaki yana nuna samun arziki ne ga dan kasuwa domin Hadisin manzon Allah (SAW) da yake cewa ga Ummu Hanee’i “Ya ke Ummu Hanee’i ki riki tumaki kiyi kiyo domin akwai albarka a cikin” Lura da wannan hadisin sai Malaman fassarar mafarki suka ce yana nuna samun arziki ne
Fassarar Markin tashi sama: Malaman Fassarar mafarki sun ce idan mutum yayi mafarkin yana tashi sama yana nuna samun daukaka ne gareshi. Wani lokaci yana nuna yawan buri ne ga mai mafarkin.
Fassarar mafarkin mai ciki ta haihi da namiji: Malaman fassarar mafarki sun ce yana nuna samun diya mace ce insha Allah
Fassarar mafarkin mutum yana karatun Fatiha: Idan mutum yayi mafarkin yana karatun Fatiha, to fassarar mafarkin yana biyan bukata ne cikin gaggawa insha Allah. Idan mutum bashida lafiya, to yana nuna zai warke daga ciyon insha Allah.