Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka (NCDC) a Nijeriya, Dr. Jide Idris, ya shirya taron gaggawa tare da Kwamishinonin lafiya na jihohin Sokoto da Kaduna da Zamfara akan wata cuta da ba’a gano kanta ba, da ta bullo a jihohin Sokoto da Zamfara. Takaddar Taron Haihuwa tare da Ba a sani ba Ciki a cikin Sakkwato da Kamfare.
Inji sanarwan da Cibiyan ta fitar ranar Jumma’a, a taron wanda aka gudanar a ranar Talata a hedkwatar NCDC a Abuja, shigaban Chibiyar ya yi magana da kwamishinan lafiya ta jihar Zamfara ta wayar tarho.
Sanarwar ta ce Idris da kwamishinonin sun tattauna yanayin da jihohin ke ciki da kokarin da sukayi domin shawo kan cutan tare da daukan matsayi akan hanyoyin da ya dace a dauka domin hana yaduwan cutan, wanda ake zargin ya auku ne saboda ayyukan hakar ma’adinai.
“Zuwa yau, mutun 196 ne suka kamu da wannan ciwon kuma mutun bakwai daga ciki sun rasa ransu a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da Ilella na jihar Sokoto. Yanzu haka ana jiran sakamako na gwaje-gwajen da aka kai a ma’aikatun NIPRID da NAFDAC da NIMR.
A KARANTA LABARIN DA HARSHEN TITANCI NCDC holds ‘emergency meeting’ over unknown illness in Sokoto
“Saboda rahotonnin da aka samu na irin wannan cutar a jihar Zamfara, za a tura wata ayarin a wannan makon domin nazarin al’amarin da kuma taimakawa,” sanarwar tace.
Hukumar NCDC tayi kira ga kauyukan da cutan ya shafa da kuma wasu kauyukan da suka jibinci wadannan, musamman a jihar Kaduna, da su kai rohoto idan suka ga alamun wannan cutar. Alamun da suka hada da zazzabi da kumburan ciki da amai da raguwar nauyi zuwa hukumar lafiya da ke kusa ko kuma a kira lambar wayan cibiyar NCDC mail amba 6232.
Haka kuma anyi kira ga ma’aikatan lafiya su kai rohoton zargin aukuwar wannan ciwon zuwa ga shugaban cibiyoyan zazari da sanarwar cututtuka na kananan hukumomi da jiha ko kuma shugaban kula da cututtuka ta jiha.
A ranar daya ga water Afrilu ne Kwamishinan lafiya ta jihar Sokoto, Asabe Balarabe ta bayyanar da aukuwar wannan cuta a karamar hukumar Isa, inda ta bayyana rashin jin dadin ta akan rashin bayyana wa Hukumarta aukuwar cutar.
“The information received showed approximately 35 suspected cases were recorded in Isa local government, yet no official from the LG Council has reported the cases to the state authorities,” she lamented.
“Bayanin da muka karba ya nuna cewa kusan mutun talatin da biyar sun kamu da wannan cuta amma duk da haka, babu wani jami’in hukuma a karamar hukuman da ya sanar mana da aukuwar wannan cuta,” Aisha tace.