Kungiyar Dalibban Najeriya da hadin gwiwar Kungiyar Matasan Arewa a yau sunyi wani gangami domin karrama Malam Ibrahim Rilwan Mohammed, Shugaban Gidauniyar IRM dake Abuja.
Taron ya samu hallatar mutane daga kowanne bangare wadanda suka hada da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da matasa da kuma dalibban daga manyan makarantu gaba da sakandare dake kowanne lungu da sako na kasarnan.
A cikin jawabinsa Mataimakin Shugaban Majalisar Dalibban Najeriya Kabiru Aminu ya bayyana cewa an zabi wanda za a karramawar ne saboda dimbin gudumuwarsa ga ci gaban dalibban da kuma matasan Najeriya a kowanne mataki.
Bugu da kari ya bayyana namijin kokarin wanda aka karrama wajen sha’anin kyautata rayuwar mata da matasa ta hanyar sana’o’in hannu domin su kasance masu dogaro ga kawunan su a cikin garuruwan su, ya kuma gayawa taron irin kyakkyawar rawar da gidauniyar sa take takawa wajen daukaka Kalmar Allah ta hanyar ginin Masallatan Jumma’a da na Hamsar Sallawati da kuma Makarantun Islamiyya a birane da karkara a kowanne yankin dake cikin kasarnan da kuma Nijar. Ya bayyana Malam Ibrahim Rilwan Mohammed a matsayin mai tsoron Allah da gudun duniya kari ga karimcinsa musamman ga marasa galihu.
A KUMA KARANTA NCDC ta gudanar da taron gaggawa don gano wata cuta da ta bayyana a Sokoto
A nashi jawabin Shugaban Kungiyar Matasan Arewa (Arewa Youth Forum for Liberty) Abdulmalik Zakari ya bayyana cewa kungiyar tayi bincike mai zurfi wajen tantace mutane masu kokari da dawainiyar mutane ba tare da gajiyawa ba.
Ya kara da cewa samun irinsa ya yi wuya a yankin Arewa balle kuma a kasar bakidaya. Ya bayyana cewa Lambar Yabon da Sarautar Garkuwan Matasan Arewa za su karfafa masa gwiwa domin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan alheri domin wasu su yi koyi dashi.
A cikin jawabinsa wani malamin Addinin Musulunci Farfesa Mansur Yalwa ya shawarci sabon Garkuwan Matasan Arewa da ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri domin Allah ba domin fadanci ba. Ya yabawa wadanda suka shirya taron saboda karrama mutane irin su Malam Ibrahim Rilwan Mohammed da su ke bayar da babbar gudumuwa wajen daukaka Kalmar Allah musamman abinda ya shafi sha’anin Ilimin Addinin Musulunci da Ilimin Zamani a kowanne mataki.
Da yake jawabi Shugaban Gidauniyar IRM kuma sabon Garkuwan Matasan Arewa Malam Ibrahim Rilwan Mohammed ya bayyana godiyarsa ga Kungiyar Dalibban Najeriya da Kungiyar Matasan Arewa da suka zabe shi domin bashi Lambar Yabo da Sarautar Garkuwan Matasan Arewa. Ya bayyana cewa a matsayin sa na Musulmi ya yi daidai ya taimakawa mutane saboda yana daya daga cikin koyarwar Musulunci, ya bayyana cewa saboda haka yake taimako saboda Allah.
Ya bayyana cewa a shigo wani lokaci da mutane ba su taimakon makota KO ‘yanuwan su, kuma idan an ga wani na taimakon al’umma sai a danganta haka da cewa yana son wani mukamin siyasa ne. “Ina tabbata maku cewa ba domin siyasa ko son wani mukamin siyasa nake yin wannan taimako ba”.