Rukayya Muhammad Fema, wata ɗaliba daga jihar Yobe, ta zama gwarzo a duniya a gasar TeenEagle Global Finals 2025, inda aka buga a London, Ingila. Ta zama ta farko wajen kwarewar amfani da harshen Ingilishi — English Language Skills.
Ta samu wannan matsayi na gasan harshen Ingilishi ne bayan ta yi gogayya da ‘yan wasa daga ƙasashe 69, cikin waɗanda suka yi rajista fiye da 20,000 daga duniya baki ɗaya.
Ita ce wakilin Najeriya ta Nigerian Tulip International College, Yobe, wacce kuma ta dumƙule wannan nasara da ƙoƙari da ƙwazo.
KALLI BIDIYON ANAN
ALSO READ TeenEagle Global finals: Yobe to honour Nafisa, Rukayya
A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi alƙawarin shirya babban taron yabo da girmamawa ga waɗanda suka taimaka matuƙa, ciki har da iyalan Nafisa da Rukayya makarantar da ta wakilta.
Haka nan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna farin cikin Najeriya gabaɗaya bisa wannan nasara ta ilmantarwa da ƙwarewa a fannin harshe.

![[BIDIYO] Yadda na lashe gasa ta duniya a fannin Ingilishi – Rukayya ‘yar shekara 17 Nafisa Aminu TeenEagle](https://ashenewsdaily.com/wp-content/uploads/2025/08/Nafisa-Aminu-TeenEagle.jpg)