Ya kamata a saka baki ga saɓanin da aka samu tsakanin ma’aikatan Hukumar Kafafen Yaɗa Labarai ta Jihar Sakkwato da Wani Babban Malamin Addinin Musulunci a Babban Filin Jirgin Sama na Sakkwato lokacin hidimar ɗaukar alhazzai.
Ya dace Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Sakkwato da Ƙungiyar ‘Yanjarida ta Ƙasa Reshen Jihar Sakkwato da Ma’aikatar Lamuran Addini ta Jiha jagororin malaman Addinin Musulunci na Sakkwato da sauran magabata da suka dace, su yi tsaye a sasanta.
Haƙiƙa, idan dai abinda kowane ɓangaren ya faɗi ya tabbata, to an sami kurakurai daga dukkan sassan biyu. Ashe kuwa bai kamata ba muhimman hukumomi na gwamnatin Jihar Sakkwato da ƙungiyoyi da dattijan da suka dace, su zura ido manyan jagorin na ci gaba da cin mutuncin junansu ta kafafen sadarwa masu dogon zango (social media) da masu gajeren zango (mainstream media).
Cigaban saɓanin na da illa ga ƙimar shugabannin da ta jama’arsu. Haka ma, ya dace masu ba Gwamnatin Jihar Sakkwato shawara da ita kanta Gwamnatin a rinƙa gaggauta ɗaukar mataki ga irin waɗannan matsalolin idan suka taso, ba a zura ido sai abu ya ɓaci irin haka ba.
Ɗanjarida da Malamin addini dukkan su suna da tasiri cikin al’umma kuma kusan ayukansu na da nasaba ta kai tsaye da juna musamman wajen faɗakarwa da ilmantarwa da seta al’umma daga hagu zuwa dama kazalika da gargaɗi ya zuwa ga ayukan alheri. Da fatar za a duba.
Muhammad Sajo