A ranar lahadin data gabata 16 ga watan maris ta shekarar 2025 wadda tayi dai dai da 16 ga watan Ramadan Kareem’, Dan Majalisa ya rabawa dubban Al’umomin kananan hukumomin Funtuwa da Dandume kayan masarufi kyauta kayan sun hada da shinkafa da Gero da masara da sauran kayan amfanin yau da kullum domin samun saukin gudanar da Azumin watan Ramadan Kareem kyauta
Daga Abdullahi Sheme
An gudanar da taron ne a dakin taro na Thirty House dake Funtuwa a jahar katsina” A nashi jawabin Shugaban jam’iyar APC na Karamar hukumar Funtuwa Barista Muhammad ya yabawa Dan Majalisa wajen kokarinshi na inganta rayuwar Al’ummar da Kuma irin jajircewar da yake dashi wajen kawo abubuwan arziki a mazabarshi yace a gaskiya wannan Dan Majalisa yayi kokari sosai ganin irin kayan masarufin daya kawo a rabawa dubban jama’a kyauta Kuma masu inganci da yawa domin irin yadda buhunan suka cika a gaskiya abin a yabane Kuma yà ciri tuta wajen raba kaya masu yawa da inganci sannan yayi kira ga jama’ar da suka amfana da suci gaba da yin Addu’ar samun zaman lafiya a yankunan su da godiya ga wannan Danmajalisa namu domin ba muyi zaben tumun dare ba sannan Yana kula da jam’iyar mu ta APC akoda Yaushe Allah ya Saka mashi da Alkhairi
Tun farko a nashi jawabin Dan Majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Funtuwa da Dandume Barista Abubakar Garba Dandume ya godewa jama’ar mazabar shi saboda irin goyon bayan da suke nuna mashi duk lokacin daya ziyarcesu wannan ya nuna mashi suna tare da shi da Kuma jam’iyar APC yace a shirye yake wajen cigaba da kawo abubuwan arziki da aiyuka masu kyau don inganta rayuwar mutanen yankin
Yaci gaba da cewar zuwan shi majalisa a kasa da Shekara 2 ya Samarwa matasa sama da 25 aiyukan yi a Gwamnatin Tarayya Kuma zai cigaba da kokarin yin hakan ya Kuma yabawa Gwamnan jahar katsina Dakta Dikko Ummaru Radda PhD Wajen kawo abubuwan arziki ga jama’ar jahar baki daya game da matsalar rashin tsaron daya dami wasu daga cikin garuruwan kananan hukumomin Funtuwa da Dandume yace zasu cigaba da kokarin kawo karshen matsalar tsaron da yaddar Allah
A nashi jawabin Shugaban jam’iyar APC na shiyyar Funtuwa Alhaji Ibrahim Danjuma yayi dogon jawabin Mai ratsa zukata yayi kira ga jama’a da suci gaba da yin Addu’ar Karin Samun zaman lafiya a yankunan kananan hukumomin su dama jaha baki daya sannan ya yabawa Danmajalisar wajen kokarinshi na inganta rayuwar mutanen mazabarshi ya Kuma fidda wadanda suka zabeshi kunya da jam’iyar APC kunya ya Kuma Kara jaddada godiyarsu ga Maigirma Gwamnan jahar katsina Dakta Dikko Ummaru Radda PhD Wajen kawo abubuwan arziki ga jama’ar jahar baki daya
Yayi kira ga sauran ‘yan majalisun Tarayya da suyi koyi da irin kyawawan aiyukan shi na Alkhairi ba shakka yau na kaddamar da kayan Alkhairi ga mutanen kirki na mazabar Funtuwa da Dandume
Ba shakka naga irin wannan abin Alkhairi wurin Danmajalisa Mai wakiltar kananan hukumomin Musawa da Matazu Alhaji Abdullahi Aliyu Dujuman Katsina shi ma Allah yasaka mashi da Alkhairi yayi koyi da Mai girma Gwamna Dakta Dikko Ummaru Radda PhD
Daga karshe a jawabin shi na godiya Alhaji Rabi’u Adamu (Kanar) ya jinjinawa Danmajalisar wajen kokarinshi da hangen nesa da Irin kokarin shi na Samarwa wasu daga cikin matasan yankin aiki a Gwamnatin Tarayya da Kuma gudanar da aiyukan mazaba daya keyi a kananan hukumomin Funtuwa da Dandume a gaskiya suna godiya kwarai da gaske daga bisani ya kaddamar da aiyukan da yayi a cikin garin Funtuwa inda aka kaddamar da ginin makarantar Islamiyya ta milyoyin Naira a Hisbuz Raheem dake layin Bakori a Funtuwa da famfo Mai amfani da hasken Rana a barikin ‘yan Sanda dake Funtuwa da ziyartar marasa lafiya da ta’aziyyar gidajen da a kayi Rashi dubban matasa ne sukuyi godiya tare da rakashi zuwa kan iyakar mahaifar Karamar hukumar shi ta Dandume