Haƙiƙa lamarin jagorancin jama’a a lokacin dimokraɗiyya yana tafiya ne da adawa. Sai dai kuma idan za a yi adawar, ya dace a yi mai ma’ana wadda hankali ke ɗauka. Lallai an yi adawa a lokacin gwamnatin Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa ta APP/ANPP (1999-2003) inda a lokacin, su Hon. Abubakar Shehu Tambuwal da Hon. Arzika Tureta (marigayi) suke a sahun gaba wajen yin adawa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP (wadda ke riƙe da gwamnatin tsakiya). Sai dai a lokacin babu kafafen sadarwa na soshiyal midiya irin yanzu. Hasali ma kila ko da akwai su, ba za a yi adawa ta wuce-wuri da cin mutuncin juna ba irin ta yanzu.
Daga Muhammad Sajo
Abinda aka al’adanta ne cewa wanda ake yi ma adawa idan ya tsima a fagen siyasa, wani sa’ilin yakan iya janye abokan adawarsa su dawo ɓangarensa. Hakan ya faru a lokacin gwamnatin Bafarawa inda ya yi nasarar janye Alhaji Abubakar Shehu Tambuwal ya dawo jam’iyyarsa. Hakan ma ta faru a lokacin Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko inda ya janye Ɗan-Madamin Isa daga wancan ɓangaren na Bafarawa zuwa nasa. Ko a haka da ake yanzu, wa ya san gobe ban da Allah (SWA)? Sarki goma zamani goma. Abinda wani shugaba kan iya jurewa na adawa, wani ba zai ɗauka ba. Kuma inda wani ya yi rawa aka yi mai kari, wani idan ya yi, kashi zai sha. A bayyane take cewa a nan jiharmu ta Sokoto, ana wuce wuri wajen amfani da soshiyal midiya gun yin adawa wadda ta ke da sigar cin zarafi da shiga rigar mutuncin juna har da na iyali. Kuma fa an lura da cewa kowane ɓangare ya sami dama, yi yake, amma ga abinda ya bayyana a halin yanzu, ɗayan ɓangaren na masu adawa ya fi zaƙewa. An tabbatar da cewa a tarihin siyasar Sokoto, ba a yi gwamna mai juriyar sukar adawa ba kamar Barista Aminu Waziri Tambuwal wanda ya sauka jiya-jiya. Me ya sa a Sokoto ba a koyi da salon adawar siyasa ta maƙwabtan jihohinmu na yankin kudu? A tasu salon adawar siyasa, iya sarrafa harshen Turanci da tajwidinsa ko akasin haka ba su ne abin suka ba ga shugaba, sai dai salon jagoranci da wanzar da shiraruwa da ayukka da ke da tasiri ga jama’a, ko bin diddigin ajandar da ɗan takara ya bayyana a lokacin neman ƙuri’un jama’a, da sauransu.
A wani ɓangaren kuma, za a iya cewa, sai bango ya tsage, ƙadangare ke samun kafar shiga. Gwamnatinmu ta Sokoto na buƙatar kimtsa gidanta musamman a haujin sadarwa (media team) saɓanin gwamnatocin da suka gabata na Bafarawa da Wamakko da Tambuwal inda kowaccensu na da gwargwadon ƙwararrin masana masu aiki kafaɗa-da-kafaɗa a haujin rubuta jawabi (speech writing team) da ababen da suka shafi fitar da bayanai (Press release) da aka tantance sosai don kauce ma tuntuɓen alƙalami da saƙo mai harshen damo da sauransu. Idan ko akwai ayarin ƙwararrin masanan (watau media team) to kila ba a ba su cikakkiyar damar yin aiki tare ba don abin ya yi armashi domin kuwa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinƙa.
Idan kuma aka zo ɓangaren ganawa da uban tafiyar, watau Gwamna, nan ma akwai buƙatar gyara sosai. A inda aka fito, lokacin da gwamnatin nan na kan turbar adawa, ganawa da Gwamna Tambuwal na ɗaya daga cikin ƙalubalolin da ake sukarsa da su domin ko komishinoninsa ba su faye samun ganawa da shi ba a lokacin da suke so. Bincike ya tabbatar da cewa duk kanwar ja ce domin babu banbancin jiya da yau inda hasali ma, ko hadiman Gwamna Dokta Ahmad Aliyu mai ci yanzu, shakku suke wajen yi ma mutum iso (ko booking) ɗin ganawa da shi. Sai kuwa idan shi Gwamnan ne ke da buƙata da ganinka. Haka abin ya ke ga muƙarraban gwamnatin, domin kuwa ƙalilan daga ‘yan majalisar Jihar ke da juriyar sauraren jama’arsu a ofis ko a gida kamar yadda ya dace. Wannan ya saɓa ma a ƙalla gwamnoni biyu da aka yi kafin Tambuwal da Ahmad. Domin kuwa ana iya ganawa da Bafarawa a ofis ko gida a wancan lokacin da yake Gwamnan Jihar Sokoto.
ALSO READ [VIEWPOINT] Ex-raying the Pathetic State of the Public Media in Sokoto
Shi Aliyu Wamakko sha-kundum ne domin kusan kowa na iya ganawa da shi a ko ina ta kama sa’ilin da yake gwamna. Ashe kuwa kyawon ɗa ya gadi ubansa. Ai ba kowa ne zai ce sai ya gana da Gwamna ba, sai wanda ke ganin matsayinsa ya kai. Wannan sanken ne ke kawo shakku ga manyan ‘yan bokonmu da sauran masana a Sokoto da ke da zimmar zuwa don bayar da shawara ga Gwamnan ko ‘yan majalisarsa. Akwai ma bayanan da ke nuna cewa galibin komishinonin gwamnatin nan ta Sokoto ba su ɗaukar waya ko da ta wanda suka sani ce. Da fatar za a gyara.
Allah Ya taimaki Jiharmu ta Sokoto, Ya magance muna matsalar tsaro a nan gida da dukkan jihohinmu da ƙasarmu Nijeriya baki ɗaya, amin.
Sajo Dan Jarida ne kuma Malami a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto